Muhammadu BuhariMuhammadu Buhari G.C.F.R.(An haife shi a ranar Sha bakwai 17 ga watan Disambar shekara ta alif ɗari tara da arba'in da biyu shekarar (1942) miladiyya. Muhammad Buhari ya kasance tsohon soja ne mai ritaya, kuma tsohon shugaban ƙasar Najeriya, sannan kuma dan siyasa ana masa lakabi da Baba Buhari Mai gaskiya. Ya zama zababben shugaban ƙasar Najeriya ne a zaben shekarar dubu biyu da sha biyar (2015) a karo na farko, lokacin da yake ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin jam'iyyar siyasar Najeriya wato APC (ALL PROGRESSIVE CONGRESS), ya kada tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan. Buhari ya sake samun nasarar zama shugaban ƙasar Najeriya a karo na biyu a shekara ta dubu biyu da sha tara (2019) yayin da ya kayar da dan takarar Jam'iyyar hamayya wato Alhaji Atiku Abubakar inda ya sauka daga mulki a shekarar dubu biyu da ashirin da uku (2023) wanda Bola Tinubu ya gaje shi. Muhammad Buhari ya taba shugabancin PTF wato (Asusu na musamman don tattara Kudin Man Fetur Wanda aka fi sani da (Petroleum Special Trust Fund (PTF) wanda tsohon Shugaban mulkin soji wato Janar Sani Abacha ya bashi matsayin a lokacin mulkinsa. Sannan kuma ya taba rike Ministan man-fetur a lokacin mulkin soji na Janar Sani Abacha. (Ihayatu (talk) 21:54, 30 Mayu shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023 (UTC))
Developed by StudentB